‘Yan sandan Afrika ta Kudu sun ceto mutum 33 da aka yi safararsu a cikin wani gida

S AFRICA POL
S AFRICA POL

‘Yan sandan Afirka ta Kudu sun ceto mutum 33 da ake zargin an yi safararsu bayan da aka same su a daure a wani daki a garin Benoni na Lardin Gauteng.

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar tun da yammacin ranar lahadi, ta ce an kama mutum daya da ake zargi dangane da lamarin.

Rahotanni sun ce jami’an hukumar KwaZulu-Natal na gudanar da bincike kan wata kungiyar safarar mutane, bayan da aka yi garkuwa da wani dan kasar waje a Springfield Park, Durban, a makon jiya.

Har yanzu ba a tabbatar da shekarun wadanda abin ya shafa ba.

Rundunar ‘yan sandan ta ce nan ba da jimawa ba, wanda ake zargin zai gurfana a gaban kotu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here