‘Yan sandan Kenya sun kama wata mata da ake zargi da jefa jaririyarta ƴar watanni takwas a cikin tekun Indiya ranar Lahadi.
Shaidun gani da ido sun shaida wa kafafen yaɗa labaran kasar cewa, matar ta jefa jaririyar ne cikin teku daga wani jirgin ruwa a lokacin da ya doshi garin Mombasa da ke gabar teku.
Bidiyon yadda ake ceto jaririyar ya karade shafukan sada zumunta, lamarin da ya sa al’ummar Kenya da dama ke nuna bacin ransu ga matar da kuma jin dadin yadda aka ceto jaririyar.
Tun da farko ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta ce jaririyar tana cikin koshin lafiya a cibiyarta ta agaji.
Har yanzu dai ba a bayyana irin tuhume-tuhumen da za a yi wa matar ba.