Biyo bayan hauhawar farashin magunguna bature a Najeriya, wasu mazauna babban birnin tarayya Abuja, sun fara amfani da ganyen “agbo” domin magance cututtuka daban-daban.
Ana yin Agbo ta hanyar haɗa ganye daban-daban, da kuma saiwoyi.
Masu aiko da rahotanni sun tabbatar da hakan daga wasu kantin magani da suka ziyarta a cikin FCT inda aka ruwaito cewa wasu magungunan ba su da yawa ko kuma babu su gaba daya, kamar su Augmentin, multivitamins, Omega H3, Ventolin inhaler, da kuma maganin rigakafi na Fleming.
Wani mai siyar magungunan bature da ya nemi a sakaya sunan sa ya ce, “Kayan GlaxoSmithKline(GSK) yanzu sun yi karanci da tsada tun lokacin da kamfanin ya sanar da ficewa daga Najeriya.
“Ga kayan GSK, muna da misalin Paracetamol wanda ake siyar da kati daya akan N200, amma yanzu ya karu zuwa N400.”
A daya daga cikin manyan kantunan da aka ziyarta, Ventolin inhaler ana siyar da shi akan N8,870 akan Naira 2,000, yayin da Augmentin ke siyar da shi tsakanin N23,000 zuwa 25,000 sabanin N3,000 zuwa N5,000 da ake siyar da shi kafin fita daga GSK.
Nicholas Adah, ya bayyana yadda abokin sa ya shawarci shi da ya fara amfani da maganin gargajiya.
” Abokina ya ce na fara amfani da maganin gargajiya, kuma da na dau shawar tasa na fara samun sauki.” inji shi.
Wane magidanci mai suna Wasiu Ahmed, ya bayyana mana yadda yake son amfani na maganin gargajiya “Me ya sa zan je in kashe kuɗina naje wajen likitan chemist ya bani maganin bature, bayan ga na gargajiya mai araha zan sha kuma na warke.”
Wani direban tasi mai suna Sunny Adeniyi, shima ya ce ya gwammace ya sha maganin gargajiya domin ya yi maganin ciwonsa saboda yana da inganci da arha fiye da magungunan bature.
“Babu kudin da za a je chemist ko asibiti domin komai a Najeriya yana da tsada, gashi ba kudi muke samu ba sosai.” in ji Mista Adeniyi.