Lamunin Bankin Duniya na dala miliyan 750: Gwamnatin tarayya ta raba Naira biliyan 135 ga Jihohi 36

Coat of Arms
Coat of Arms

Gwamnatin tarayya ta raba Naira biliyan 135 da miliyan 400 ga Jihohin kasar ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja, biyo bayan nazari a karo na biyu karkashin shirin farfado da tattalin arzikin Najeriya bayan annobar COVID-19.

Kodinetan shirin NG-CARES Dakta Abdulkarim Obaje ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi ta hannun Daraktan yada labarai na shirin NG-CARES Suleiman Odapu.

Shirin na NG-CARES, wanda Bankin Duniya ya tallafa da kudi kimanin dala miliyan 750, shiri ne da ya kunshi bangarori daban-daban da nufin ba da agajin gaggawa ga marasa galihu da talakawan Najeriya.

Kazalika shirin yana mayar da hankali musamman wajen tallafa wa kananan manoma da kuma masu kanana da matsakaitan sana’o’in dogaro da kai, wadanda suka samu koma baya sakamakon annobar COVID-19.

Obaje, ya kara da cewa rabon tallafin yana da nasaba da yunkurin jahohi da kuma babban birnin tarayya Abuja a kokarinsu na taimakawa marasa galihu a karkashin shirin NG-CARES.

Sanarwar ta ce jihohin Nasarawa, Cross Rivers, da Zamfara ne suka zama kan gaba, inda suka samu Naira biliyan 13 miliyan 600 da Naira biliyan 10 da miliyan 900 da kuma Naira biliyan 10 da miliyan 200 a zagaye na biyu na tantance shirin.

Idan za’a iya tunawa tun a watan Janairun 2022, tsohon mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da shirin na NG-CARES.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here