Mutane da dama sun rasa rayuka a Kaduna bayan da Sojoji suka jefa Bam yayin Mauludi

Kaduna map
Kaduna map

Ana fargabar cewa mutane da dama sun mutu a yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna sakamakon wani harin bam da aka ce jirgin sojin saman Najeriya ya jefa a lokacin da ake bikin Mauludi a Tudun Biri.

Jaridar daily trust ta rawaito cewa, rahotannin farko na nuni da cewa kimanin mutane 30 ne suka mutu sakamakon aukuwar lamarin tun a ranar Lahadi da misalin karfe 9 na dare.

A safiyar ranar Litinin ne wani tsohon dan majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, ya wallafa wani rubutu a shafin sa na X wanda ke nuni da faruwar lamarin.

Sai dai mazauna garin da suka yi magana sun ce bam din ya tashi ne yayin da mutanen kauyen suka taru domin yin Mauludi.

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Samuel Aruwan, wanda bai bayar da alkaluman adadin wadanda suka mutu ba, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba gwamnati za ta yi jawabi ga manema labarai a gidan gwamnati.

Har kawo lokacin hada wannan rahoto rundunar sojin saman kasar nan ba ta fitar da sanarwa dangane da lamarin ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here