Rundunar sojin saman Najeriya ta saki bam a kan wasu mutane dake tsaka da gudanar da Mauludi a Kaduna

Kaduna map
Kaduna map

Ana fargabar cewa mutane da dama sun mutu a wani yanke da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna sakamakon wani harin bam da aka ce jirgin sojin saman Najeriya ya jefa a kansu lokacin da suke tsaka da gudanar da Mauludi a Tudun Biri, inji rahoton Daily Trust.

Rahoton jaridar na nuni da cewa kimanin mutane 30 ne suka mutu sakamakon sakin bam din a ranar Lahadi da misalin karfe 9:00 na dare.

A safiyar ranar Litinin ne tsohon Sanata Shehu Sani, ya wallafa wani rubutu a shafin sa na X wanda ke nuni da faruwar lamarin.

Sai dai mazauna garin da suka yi magana sun ce bam din ya tashi ne yayin da mutanen kauyen suka taru domin yin Mauludi.

“Suna bikin Mauludi ne lokacin da jirgin ya jefa bam a kansu, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 30 nan take,” in ji wani mazaunin garin.

Kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta jihar Samuel Aruwan, wanda bai bayar da alkaluman adadin wadanda suka mutu ba, ya bayyana cewa gwamnati za ta yi jawabi ga manema labarai.

“Za mu yi wa manema labarai jawabi a gidan gwamnati kan lamarin nan bada jimawa ba. Don haka, mu hadu da karfe 10 na safe,” in ji shi.

NAF dai ba ta bayar da wata sanarwa ba dangane da faruwar lamarin har zuwa  lokacin da ake hada wannan rahoto.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here