Gobara ta tashi a gidan talabijin na NTA

Fire guts NTA network centre.jpeg
Fire guts NTA network centre.jpeg

Wuta ta kone cibiyar sadarwa ta gidan talabijin na Najeriya (NTA) da ke Sokoto.

An sanar da faruwar gobarar ne a ranar Lahadi ta hanya kafar sada zumunta ta X.

A wani faifan bidiyo da aka saka kafar ta X  ya nuna hayaki na fitowa daga ginin.

Gobarar da ta kwashe sama da sa’o’i uku tana ci, sai dai  ba ta shafi dakin studio da kayan aiki da sauran wuraren da ake aiki da su ba.

Injiniyoyin na zargin cewa watakila gobarar ta tashi ne sakamakon karfin wutar lantarki.

SOLACEBASE ta ruwaito wannan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da gobara ta lalata wasu sassan gidan rediyon tarayya FRCN a Kaduna a ranar Lahadi da yamma da kuma sa’o’i 24 bayan da gobara ta kone ofishin shugaban ma’aikata a sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja ranar Asabar. wanda ya shafi Block C.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here