Zulum ya amince da fara biyan kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye

WhatsApp Image 2026 01 29 at 17.07.14 750x430

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da fara biyan kuɗaɗen rabon wata-wata na doka ga dukkan asusun ƙananan hukumomi 27 na jihar kai tsaye.

Mukaddashin gwamnan jihar, Alhaji Umar Usman Kadafur, ne ya sanar da wannan amincewa a ranar Alhamis bayan ya jagoranci rantsar da sababbin shugabannin ƙananan hukumomi 27 da aka zaɓa.

Kadafur ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Gwamna Zulum na ƙarfafa tsarin dimokiraɗiyya a matakin ƙasa, yana mai cewa an ɗauki matakin ne bisa bin hukuncin kotun koli da kuma kiran da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa gwamnonin jihohi a watan Disamba na shekarar 2025.

Ya bayyana cewa manufar hakan ita ce bai wa shugabannin ƙananan hukumomi damar samun kuɗaɗensu kai tsaye domin su gudanar da ayyuka yadda ya kamata.

Mukaddashin gwamnan ya ce shugabannin ƙananan hukumomi su kasance masu kusanci da al’ummarsu, yana mai jaddada cewa Gwamna Zulum ya himmatu wajen bunƙasa jihar Borno ta kowane fanni.

Ya ce ana sa ran shugabannin ƙananan hukumomi za su tabbatar da gaskiya da riƙon amana a duk wani kuɗi da suka karɓa, tare da bayyana cewa jihar Borno ita ce kaɗai jihar da ke bai wa ƙananan hukumomi rabon kuɗaɗensu kai tsaye ba tare da katsalandan ba.

Kadafur ya ƙara da cewa za a ci gaba da wallafa duk kuɗaɗen da ake bai wa ƙananan hukumomi a bainar jama’a domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana, tare da cewa zamanin ƙorafe-ƙorafe kan jinkirin amincewa da kuɗi daga ɓangaren gwamnati ya wuce.

Haka kuma ya umarci sababbin shugabannin ƙananan hukumomi da su ba da muhimmanci ga walwalar ma’aikatan ƙananan hukumomi tare da tabbatar da biyan albashi da hakkokinsu a kan lokaci.

Ya ce dole ne shugabannin su kula da dukkan kuɗaɗen jama’a yadda ya dace, tare da aiwatar da ayyuka da shirye-shirye bisa tsare-tsaren dabarun shekaru goma na jihar.

Bikin rantsarwar ya samu halartar babban bulaliyar majalisar dattawa, Mohammed Tahir Monguno; Sanata Kaka Shehu Lawan; shugaban jam’iyyar APC na jihar Borno, Bello Ayuba; da tsofaffin mataimakan gwamnan jihar, Ali Abubakar Jata’Au da Usman Mamman Durkwa.

Sauran mahalarta taron sun haɗa da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Jere, Injiniya Satomi Ahmad; shugaban majalisar dokokin jihar Borno wanda shugaban masu rinjaye Dige Mohammed ya wakilta; sakataren gwamnatin jihar; shugaban ma’aikatan gwamnati, Dakta Amini Muhammad Ghuluze, da sauran manyan jami’an gwamnati da na jam’iyya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here