Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Dakta Kayode Fayemi, ya musanta rahotannin da ke cewa ya gudanar da wata ganawar siyasa ta sirri da tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, a birnin Abuja.
Hakan na cikin sanarwa ta hannun Malam Ahmad Sajoh, shugaban ofishin yaɗa labarai na Kayode Fayemi, inda ya bayyana cewa labarin ba gaskiya ba ne kuma yana ruɗar da jama’a.
Sanarwar ta bayyana cewa labarin ƙarya ne tsagwaron ta, tare da kira ga al’umma da su yi watsi da abin da ta bayyana a matsayin ƙarya fili da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta.
Ta bayyana cewa iƙirarin ya bayyana ne a dandalin X, wanda aka fi sani da Twitter a baya, ta hannun wasu asusun kafafen sada zumunta, inda aka haɗa shi da wani tsohon bidiyo da ke nuna Fayemi yana gaisawa da Kwankwaso a gidansa.
Sanarwar ta jaddada cewa wannan iƙirari ba shi da tushe balle makama, kuma hakan zai ba Kwankwaso mamaki kamar yadda ya ba Fayemi mamaki.
Ta ƙara da cewa Fayemi ya taɓa haɗuwa da Kwankwaso sau ɗaya kacal cikin shekara guda, kuma hakan ya faru ne a wajen ƙaddamar da littafin tsohon Antoni Janar na ƙasa, Mohammed Bello Adoke SAN, wanda aka yi a bainar jama’a.
Har ila yau, sanarwar ta bayyana cewa Fayemi da Kwankwaso abokai ne tun lokacin da suke gwamnoni, amma dangantakar ta su ta kasance ta kashin kai ce ba ta siyasa ba, inda aka gina ta ne bisa mutunta juna da kuma kishin ci gaban Nijeriya, ba bisa wata manufa ta jam’iyya ba.
Sanarwar ta yi gargaɗi ga masu ƙoƙarin ɗora ma’anar siyasa kan dangantakar kashin kai, tare da bayyana cewa Fayemi yana da abokai da dama da ba sa harkar siyasa ko kuma ba su da alaƙa da jam’iyyun siyasa iri ɗaya.
NAN













































