Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa aikin jirgin ƙasan Abuja–Kaduna ya tabarbare matuƙa har ya kai matsayin da keke ko babur mai ƙafa uku da aka fi sani da Keke Napep ke iya kai fasinja Kaduna cikin lokaci fiye da jirgin ƙasan.
Akpabio ya bayyana haka ne yayin zaman majalisar dattawa da aka gudanar domin duba koma bayan ayyukan jiragen ƙasa a ƙasar, musamman layin Abuja–Kaduna–Kano da ya fi shahara, inda ya nuna damuwa kan tsawon lokacin tafiyar da fasinjoji ke yi a yanzu.
Biyo bayan haka, Majalisar Dattawan ta ƙaddamar da kwamitin wucin-gadi na bincike kan tsarin jiragen ƙasa gaba ɗaya a Nijeriya, wanda aka kafa a watan Nuwamba 2025, domin bincika ayyukan jiragen ƙasa a faɗin ƙasar cikin makonni shida, tare da naɗa tsohon gwamnan Jihar Edo, Sanata Adams Oshiomhole, a matsayin shugaban kwamitin.
Akpabio ya jaddada cewa lokacin da aka fara aikin jirgin ƙasan, tafiya daga Abuja zuwa Kaduna na ɗaukar kusan awa ɗaya da rabi, amma a yanzu fasinjoji na shafe fiye da awanni uku a kan layin, lamarin da ke nuna koma baya mai tsanani a aikin.
Sanata Abdul Ningi na jam’iyyar PDP daga Bauchi ta Tsakiya, ya goyi bayan wannan batu, inda ya bayyana kwarewarsa ta baya-bayan nan da ya yi amfani da jirgin zuwa Kaduna, yana mai cewa fasinjoji sun shafe sama da awanni uku da rabi a hanya saboda rashin wani zaɓi na daban.
Ya bayyana cewa tun daga shekarar 2015, jirgin ƙasan na gudanar da zirga-zirga guda goma a rana, biyar daga Abuja zuwa Kaduna da biyar daga Kaduna zuwa Abuja, tare da jigilar fasinjoji kusan 10,000 a kullum, amma adadin ya ragu zuwa tsakanin 800 zuwa 900 a rana, yayin da zirga-zirgar ta ragu zuwa sau biyu kacal a rana, abin da ya rage kuɗaɗen shiga daga kimanin naira biliyan 1.8 a wata.
Sanata Ningi ya kuma zargi cewa wasu kayan aikin da aka girke lokacin aiwatar da kwangilar jirgin ƙasan tsofaffi ne da aka riga aka yi amfani da su, abin da ya jefa Najeriya cikin asara, tare da nuna cewa jinkirin tafiyar na nuna rashin kulawa daga masu ruwa da tsaki.
Idan za a iya tunawa, gwamnatocin marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua ne suka fara aikin jirgin ƙasan Abuja–Kaduna, gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ta gada, yayin da gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ta ƙaddamar da shi bayan kammala kwangilar da aka kiyasta kuɗinta dala biliyan 1.64, inda kamfanin China Civil Engineering Construction Corporation CCECC ya gina layin mai tsawon kilomita 186.5, tare da tallafin rancen dala miliyan 500 daga bankin fitar da kaya na ƙasar China da kuma gudummawar gwamnatin tarayya.











































