Asusun lamunin ilimi na Najeriya NELFUND ya tsawaita wa’adin karɓar buƙatun neman rancen karatu na zangon karatu na 2025/2026 daga ranar 31 ga Janairu zuwa ranar 27 ga Fabrairu.
Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa na dabaru na asusun, Oseyemi Oluwatuyi, ya fitar a birnin Abuja, inda aka bayyana matakin a matsayin ƙoƙarin bai wa masu neman rancen ƙarin lokaci domin kammalawa da tura buƙatunsu.
Oseyemi Oluwatuyi ya bayyana cewa tsawaita wa’adin an yi ne domin tabbatar da cewa babu ɗalibin da ya cancanta da za a bari a baya sakamakon ƙarancin lokaci, tare da sauƙaƙa wa masu nema damar kammala dukkan matakan da ake buƙata.
Daraktan gudanarwa na NELFUND, Akintunde Sawyerr, ya bayyana cewa wannan mataki na nuna ƙudurin asusun wajen faɗaɗa dama da tabbatar da samun rancen ga dukkan ɗaliban Najeriya da suka cancanta.
Ya kuma bayyana cewa tsawaita wa’adin zai bai wa waɗanda ba su kammala buƙatunsu ba ko kuma ba su fara ba damar amfana da shirin, tare da tabbatar da cewa dukkan bayanan da ake buƙata sun isa kafin ranar 27 ga Fabrairu.
Ya ƙara da cewa asusun zai ci gaba da fitar da ƙarin bayani da sabuntawa ta hanyoyin sadarwar sa na hukuma, domin tabbatar da isar da sahihin bayani ga jama’a.
NAN













































