Barazanar tsaro: An rufe hanyoyin da ake bi ana wuce wa ta kusa da gidajen gyaran hali na Kurmawa dana Goron dutse a Kano

download
download

Yanzu haka dai hanyoyin da ake bi ana wuce wa, ta kusa da gidajen ajiya da gyaran hali na unguwar Kurmawa dana Goron dutse sun kasance a rufe tun da safiyar Juma’ar nan.

Kan haka wakilin mu Abubakar Sabo ya tuntubi mai magana da yawun hukumar a nan Kano, DSC Musbahu kofar Nassarawa wanda ya shaidawa cewa, sun yi hakan ne dan kara tabbatar tsaro ga gidajen da kuma wadan da ke zaune a ciki.

Ya kuma Kara da cewa ɗaukar matakin ya biyo abubawan da suka faru a gidan gyaran hali na Kuje dake Abuja dama sauran wasu wuraren.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here