Na ki daukar Wike ne saboda ba zan ji dadin aiki da shiba-Atiku Abubakar

atiku abubakar
atiku abubakar

Dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya ce ya ki daukar Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas a matsayin mataimakinsa ne saboda yana son ya dauki mutumin da zai “ji dadin aiki da shi”.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a hira ta musamman da ya yi da gidan talbijin na Arise TV ranar Juma’a.

Dan takarar na PDP ya dauki gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa a zaben 2023, duk da cewa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP ya ba shi shawarar daukar Wike.

Da yake magana game da matakin da ya dauka na zabar mataimakinsa, Atiku ya ce ya dauki Okowa maimakon Wike ne saboda yana son mutumin zai iya “gabatar da tsare-tsaren jam’iyyarmu, kuma wanda zai iya hada kan ‘yan kasa”.

“Ban yi watsi da Gwamna Wike ba. Babu wanda aka yi watsi da shi a jam’iyya. Amma dole ka fahimci cewa hurumin dan takara ne ya zabi mataimakinsa — mutumin da ya yi amannar cewa zai yi aiki da shi cikin lumana, kuma wanda zai gabatar da manufofin jam’iyya, kuma ya yi kokarin hada kan kasa,” in ji Atiku.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here