Zaɓuka masu inganci su ne ginshikin makomar Najeriya – Dapo Olorunyomi

WhatsApp Image 2025 12 06 at 05.44.31 750x430

Mawallafin jaridar Premium Times kuma mamallakin kungiyar cibiyar CJID Mr Dapo Olorunyomi ya bayyana cewa dole al’umma su fifita zaben shugabanni masu gaskiya, kwarewa da hangen nesa domin kafa tubalin ingantaccen mulki.

Dapo ya yi wannan bayani ne a matsayin shugaban taro da aka gabatar a jami’ar Tarayya da ke kashere a jihar gombe ranar Alhamis, inda Farfesa Attahiru Muhammadu Jega ya yi nazari kan zabe da kyakkyawan mulki a kasar nan a gaban manyan baki da dalibai.

Olorunyomi ya yaba wa mataimakin shugaban jami’ar FUK Farfesa Umaru Pate bisa irin ci gaban da jami’ar ta samu, yana mai bayyana ginin jami’ar a matsayin abin burgewa da ke nuna yadda jagoranci mai hangen nesa ke kawo cigaba mai dorewa.

Ya ce irin wannan ci gaba da FUK ta samu na nuna cewa idan aka samu shugabanci mai tsari da hada kan al’umma Najeriya na iya bunkasa, tare da samar da damar ci gaban kowa ba tare da wariya ko fifikon kabilanci ba.

Karanta: Tsarin Demokradiyyar Najeriya na cikin haɗari idan babu sahihin zaɓe – Jega

Yayin da ya koma kan taken jawabin, ya jaddada cewa zabe mai inganci shi ne ginshikin kyakkyawan mulki, inda ya nuna cewa duk da cigaban da hukumar Zaɓe ta samu ta fuskar tsarin amfani da na’urar BVAS da IREVE, kalubalen siyasar gwamnati, matsalolin tsari da kararrakin kotu na rage amincewar jama’a ga sakamakon zabe.

Olorunyomi ya kuma jaddada cewa duk da wadannan matsaloli akwai alamun cigaba musamman ta bangaren matasa, kungiyoyin farar hula, ’yan Najeriya mazauna ketare da jaridu masu bin diddigi, wanda ke tayar da murya wajen karfafa ingancin tsarin Dimokuraɗiyya.

Ya ce Zaɓe da kyakkyawan mulki su ne ginshikin rage talauci, samar da tsaro, bunkasa aiki, inganta ilimi da karfafa hangen nesa na kirkire-kirkire, yana mai jan hankalin al’umma zuwa ga zaben shekarar 2027 sakamakon mahimmancinsa ga makomar kasar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here