Kungiyar Amnesty International ta soki matakin kamawa da rundunar ’yan sanda ta yi wa tsohon shugaban hukumar karɓar ƙorafi da yaki da cin hanci ta kano Muhuyi Magaji Rimin Gado, tana mai cewa lamarin ya sabawa tsarin doka da ka’idar kare hakin jama’a.
Kungiyar ta bayyana cewa rundunar ’yan sanda ta isa ofishin aikinsa da ke birnin kano dauke da manyan makamai, inda ta gudanar da kamen cikin yanayi na tsoratarwa da hana shiga tsakani ga kowa.
Kungiyar ta ce kamen ya samo asali ne daga umarnin babban Sufeton ’yan sanda, wanda hakan ke nuna cigaba da daukar matakai ba tare da mutunta tsarin mulki da ka’idar bin doka ba.
Kungiyar ta tunatar da cewa a watan Janairu jami’an sa ido daga ofishin babban Sufeton ’yan sanda sun kama Muhuyi Magaji saboda binciken da ya gudanar kan zarge-zargen cin hanci a lokacin mulkin Abdullahi Ganduje, wanda ya haifar masa da cigaba da matsin lamba kan aikinsa.
Labari mai alaƙa: Yanzu-yanzu: ’yan sanda sun kama tsohon shugaban hukumar karɓar ƙorafi da yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano Muhuyi Magaji Rimin Gado
Kungiyar ta bayyana cewa amfani da rundunar ’yan sanda wajen danniya da tauye hakin jama’a ya saba wa tsarin mulki, kuma dole ne hukumar ta bi doka wajen duk wani mataki da take dauka.
Kungiyar ta nemi a saki Muhuyi Magaji Rimin Gado ba tare da wani sharadi ba, tana mai cewa cigaba da tsare shi saboda aikinsa na yaki da cin hanci tarnaki ne ga martabar kasa da tsarin adalci.












































