
Babban bankin kasa CBN ya bawa abokan hulda masu ajiyar kudi a bankunan kasar nan tabbacin cewa babu abinda zai samu kudaden su.
The Acting Director, Corporate Communications Department of the CBN, Mrs Hakama Sidi-Ali, gave the assurance in a statement on Wednesday.
A cikin wata sanarwa da mukadishiyar daraktar yada labaran bankin Hakama Sidi-Ali ta bada tabbacin a cikin wata sanarwa da ta fitar da safiyar larabar nan.

Karanta wannan: Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya rasu
A cewarta, tabbacin ya biyo bayan rahoton amincewar gwamnatin tarayya cewa za ta ci gaba da kula da wasu bankunan kasuwanci, wanda babban bankin ke yi a baya.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa akwai wani rahoto da ba’a tabbatar da sahihancinsa ba, da kafafen yada labarai ke yadawa cewa CBN zai ci gaba da kula da bankunan Union da Keystone.
Ana danganta zargin hakan ne da wani rahoto da Jim Obazee, mai bincike na musamman na CBN ya fitar, na cewa tsohon gwamnan babban bankin kasar nan Godwin Emefiele, ya yi amfani da abokan huldarsa wajen sayen bankunan kasuwanci 2.












































