Barau Ya Mika Ta’aziyar Sa Ga Iyalain Tsohon Kakakin Majalisar wakilai, Ghali Na’Abba

Senator Barau Jibrin
Senator Barau Jibrin

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya jajanta wa tsohon kakakin majalisar wakilai, Alhaji Ghali Umar Na’Abba, wanda ya rasu a ranar Laraba, yana da shekaru 65 a duniya.

Sanata Barau, a cikin sakon ta’aziyyar mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ismail Mudashir ya yi addu’ar Allah SWT ya baiwa Marigayi Kakakin Majalisa Jannatul Firdausi da duk wadanda ya bari ikon jure wannan rashi mara misaltuwa.

Sanata Barau, a lokacin da yake jinjina wa marigayi kakakin, ya ce marigayin kwararre ne na majalisa, wanda ya ba da goyon baya da kuma kare ‘yancin ‘yan majalisa a zamaninsa na shugaban majalisar wakilai tsakanin Yuli da Yuni 2003.

Na’Abba wanda ya wakilci Kano Municipal tsakanin 1999 zuwa 2003 ya zama kakakin majalisar bayan Alhaji Salisu Buhari ya yi murabus daga mukamin.

Mataimakin shugaban majalisar dattijai wanda ya jagoranci kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai a zamanin Na’Abba, ya ce marigayin ya jajirce wajen ganin an raba mukamai, da kare doka da kuma kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya a lokacin mulkinsa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here