Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya rasu

Akeredolu
Akeredolu

Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya rasu.

A cewar majiya daga iyalan sa, Akeredolu ya rasu ne ranar Laraba a Lagos, yana da shekaru 67 a duniya.

Rahotannin sun bayyana cewa marigayin ya rasu ne da misalign karfe 2 na daren Larabar nan.

Karanta wannan: Shugaba Tinubu ya damu da wahalhalun da ake ciki-Abdul’aziz

Jami’an gidan gwamnatin jihar ta Ondo sun ce gwamnan ya rasu ne a wani asibiti da yake karbar magani a Jamus.

Ya rasu ne bayan ya shafe lokaci yana fama da cutar kansar jini da kansar mafitsara.

Rasuwar tasa na zuwa ne kimanin mako biyu, bayan da ya rubuta wasikar tafiya neman lafiya, inda ya mika ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

Kafin sannan an yi ta dambarwar siyasa a jihar Ondo, inda ‘yan majalisar jihar suka yi yunkurin tsige mataimakin daga kujerarsa, amma daga bisani Shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani.

Gwamnan dai ya shafe kusan wata uku a kasar Jamus yana jinya, daga bisani ya dawo Najeriya a watan Satumba.

An zabi Akeredolu a matsayin gwamnan jihar Ondo a wa’adi na biyu a shekara ta 2020.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here