
Babban mataimaki na musamman ga shugaba kasa kan harkokin yada labarai, Abdulaziz Abdulaziz, ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya kasance mai tausayi kuma ya damu da halin kuncin da ‘yan Najeriya ke ciki.
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da shugabannin gidajen rediyo da mawallafa jaridu da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum ranar Litinin a Kano.
Abdulaziz ya bayyana cewa shugaban kasar na sane da irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta sakamakon manufofin gwamnati daban-daban.
Ya kuma yi nuni da cewa gwamnati na kokarin rage wa ‘yan Najeriya matsin rayuwa.
A cewarsa, domin dakile wahalar cire tallafin mai ga jihohi, gwamnatin tarayya ta bayar da Naira biliyan 5 ga kowace jiha da kuma manyan motocin hatsi.
Ya ce tuni duk jihohin sun karbi Naira biliyan biyu daga Gwamnatin Tarayya.
Abdulaziz ya bayyana cewa an kuma fitar da kudade don siyan rukunin motocin bas masu amfani da lantarki.
Ya ci gaba da cewa, shugaban ya kuma amince da ba da lamuni na dalibai domin samun saukin ilimi ga daliban manyan makarantu.
Abdulaziz, wanda ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya, ya ce shugaban ya baiwa harkokin tsaro fifiko.
Ya kuma tabbatar wa da ‘yan jarida cewa, a ko da yaushe shugaban kasar zai kare ‘yancin yada labarai da mutunta ra’ayoyi mabambanta
Shugaban ya bukaci kafafen yada labarai da su tallafa tare da inganta kyawawan manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
Abdulaziz ya ce kafafen yada labarai bisa ga irin rawar da suke takawa da ayyukansu, wata hanya ce da za ta ci gaba da dora gwamnati a kan turba ta gaskiya.
Karanta wannan: Tsohuwar ministar jin ƙai ta yi martani kan zargin ta da ake da almundahanar naira biliyan 37
Yayin taron mawallafin jaridar Solacebase, Malam Abdullateef Abubakar Jos ya bukaci mai taimaka wa shugaban kasar da ya ci gaba da gudanar da zaman tattaunawa ta yadda za a samu ci gaba mai dorewa tsakanin fadar shugaban kasa da ’yan jarida domin a rika tantance bayanan da ba su dace ba.
Abdullateef Jos ya yi amfani da damar wajen ya bawa shugaba Tinubu bisa zabar AbdulAziz AbdulAziz a matsayin mai taimaka masa duba da irin gudunmawar da ya bayar wajen aikin jarida.
A nasa jawabin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa wato NUJ, reshen jihar Kano, Alhaji Abbas Ibrahim ya bukaci ‘yan jarida da su kara kaimi a ayyukansu.
Ya kuma yi kira gare su da su kasance masu jajircewa da kirkira a duk abin da za su yi domin a halin yanzu aikin ya kasance sai mai kwazo.
Ibrahim ya kuma bukaci ‘yan jarida da su yaki yada labaran karya, tare da inganta manufofin gwamnati, da kuma tunawa gwamnati nauyin jama’a dake wuyan su.
Shugaban ya ce, babu shakka Abdulaziz ya bayar da gudunmawa sosai wajen bunkasa aikin jarida, kuma ba za a iya mantawa da nasarorin da ya samu ba.