A ranar Laraba ne Majalisar Dattawa ta tabbatar da Ola Olukoyede a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC).
Majalisar ta kuma tabbatar da nadin Muhammad Hammajoda a matsayin sakataren hukumar yaki da cin hanci da rashawa.
Tabbatar da mutanen biyu ya biyo bayan tantance su ne da babban zauren majalisar ya yi a ranar Laraba da yamma, kimanin mako guda bayan da shugaba Bola Tinubu ya nada su.
Majalisar ta kuma tantance tare da tabbatar da nadin Halima Shehu a matsayin shugabar hukumar kula da harkokin zuba jari ta kasa (NSIPA).