An tattaro cewa gwamnonin G-5 sun gana da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke Abuja jim kaɗan bayan kammala taronsu a gidan Wike.
Ministan Abuja ne ya jagorance su zuwa wurin shugaba Tinubu, sai dai har yanzu ba bu cikakkun bayanai kan batutuwan da suka tattauna da shugaban ƙasa.
Amma wasu rahotanni sun nuna cewa taron ya maida hankali ne kan alaƙa ta aiki da ta haɗa shugaba Tinubu da gwamnonin G-5 na PDP wanda ya samo asali tun kafin zaɓen 2023.
Wata majiya a taron wanda ta nemi a sakaya sunanta saboda ba ta da izinin yin magana kan batun ta ce: “A farko Gwamnonin PDP na G-5 sun gana a gidan Wike na ‘yan sa’o’i kafin daga bisani su wuce Villa domin ganawa da shugaban ƙasa.
Ba ni da cikakken bayani game da abin da aka tattauna a halin yanzu.”












































