A ranar Juma’a ne gwamnatin jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira biliyan 1.4 don ginawa da kuma gyara masallatai da makabartu a fadin jihar.
Mista Sagir Musa, kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu, ya shaidawa manema labarai a Dutse cewa majalisar zartarwa ta jiha ce ta amince da kashe kudin.
Ya kara da cewa, za a yi amfani da wani bangare na kudaden ne wajen gina fadojin Hakimai. A cewar kwamishinan.
(NAN)













































