Shugaba Bola Tinubu, a karshen mako a Guinea-Bissau, ya ce Najeriya ta kuduri aniyar kiyaye zaman lafiya da tabbatar da dorewar dimokuradiyya a yammacin Afirka.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa Dele Alake, ya fitar a karshen mako.
Shugaba Tinubu ya ce Najeriya za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na sa ido wajen karfafa dimokradiyya kamar yadda ta yi a kasashen Laberiya da Saliyo.
“Najeriya kasa ce da ta yi fice a Saliyo da Laberiya da sauran wurare,” in ji shi.
Ya godewa sojojin da kwamandan su, Janar Al-Hassan Grema, bisa sadaukarwa da hidimar da suke yi wa Najeriya da kuma kasar da ta karbi bakuncinsu.
A nasa bangaren, Birgediya Janar Grema ya bayyana jin dadin sojojin ga Shugaba Tinubu kasancewarsa babban kwamandan na farko a tarihin Najeriya da ya ziyarci sojojinsa a kasashen waje.
Tun da farko, jirgin shugaban ya sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa da ke birnin Bissau da misalin karfe 5:30 na yamma agogon kasar gabanin taron kungiyar ECOWAS, wanda shi ne karon farko da ya shiga kasar Afrika ta kudu tun bayan hawansa karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Ana sa ran shugabannin yankuna 16 da ke halartar taron za su yi shawarwari kan batutuwa biyar masu muhimmanci a yankin.
Sauran batutuwan da za a yi la’akari da su sun hada da rahoton halin da ake ciki a Jamhuriyar Mali, Burkina Faso da Guinea, da takardar sheda kan shirin bai wa kungiyar ECOWAS kudin bai daya da kuma rahoton cikas ga ‘yancin zirga-zirgar kayayyaki a kan hanyar Abidjan zuwa Legas.
Sanarwar ta kara da cewa ana sa ran shugaba Tinubu zai dawo Najeriya ranar Litinin mai zuwa.