Yayin da lamura ke kara tabarbarewa, ake ci gaba da yiwa mutane fashin wayoyin hannu a jihar Kano, gwamnati ta bayyana matsayarta kan fashin.
A cewar gwamnati, daga yanzu ya zama doka cewa, kwacen waya na daidai da fashi da makami, kuma za a huunta duk wanda aka kama.
Wannan na nufin cewa, duk lokacin da aka kama dan kwacen waya, za a yi masa hukunci ne daidai da wanda kotu ke yiwa ‘yan fashi da makami.
Wannan batu na fitowa ne daga bakin kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba da sanyin safiyar ranar Asabar 27 ga watan Mayu.
A cewar kwamishinan, an dauki matakin alanta kwacen waya a matsayin ta’addancin fashi da makami ne biyo bayan taron majalisar zartaswa da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta.
Ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta fahimci cewa, yawaitar kwacen waya da jikkata mutane a jihar babban abin damuwa ne da bai kamata a bari ya ci gaba da faruwa ba.
Hakazalika, ya ce tabbas za a dauki tsauraran matakai na ganin an dakile ci gaba da aukuwar lamarin a yankuna daban-daban na jihar. Idan baku manta ba, mazauna jihar Kano sun shiga matsanancin damuwa game da yadda ake yawan tare mutane da wukake ana kwace musu wayoyi.













































