Emefiele Ya Shiga Ganawa Da Tinubu A Aso Rock

BREAKING
BREAKING

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, yanzu haka yana Fadar Aso Rock don ganawa da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

Tinubu dai ya shiga fadar ne wajen misalin karfe 2:30 na rana

A ranar Litinin ce aka rantsar da Tinubu a matsayin Shugaban Najeriya na 16.

Ya sami tarba daga Mataimakinsa, Shettima, Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele; Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mele Kyari da Shugaban Majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da kuma Babban Sakataren Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Tijjani Umar da Wale Edun da kuma James Faleke.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here