Dalilin da yasa banje rantsar da Abba Gida Gida ba – Ganduje

Abdullahi Ganduje Kano 1 1
Abdullahi Ganduje Kano 1 1
Gandujen ya shaidawa a hakane a wata hira da ya yi da BBC Hausa, inda ya ce bashi da wata matsala da sabowar gwamanatain ta kano.
Ya kara da cewa “Mika mulki ya kasu gida biyu, na farko shine mika mulki wanda ya kunshi bada  takardu da duk wani bayanai na gudanarwar gwamnati, wanda ya hada da aiyukan ada aka agama da wanda ma ba’a gama ba, da kuma shawar-ware da ake bawa gwamantin da za’a rantsar.”
“Kashi na biyu kuma shine rantsuwa. Indan gwamanatin da zata tafi idon ba jama’iyyar su daya da wacce za’a rantsar ba, ya zama dole kada a halarci taron rantsuwar domin tsoron samun hatsaniya a tsakanin magoya bayan mu.”
Ya yin da aka tambaye shi akan ko ya zo rantsar da Tinubu ne domin neman mukami, sai Gandujen ya ce ” Ni ban zo nan saboda neman mukami ba, amma idon aka bani zan karba”

“Ina kyuatatawa gwamnatin Tinubu zato. kuma muna yi masa addu’a samun nasara a gwamnatin sa, kuma zamu cigaba da bashi taimako domin an zabe shine sabo da ya shuka abin alkairi a baya.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here