Halin da ake ciki yayin da wani abu ya fashe a Barikin Giwa da ke Maiduguri – Majiyoyin tsaro

Gp0u0vUXgAAjhIp 675x430

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa wani abun fashewa ya fashe a barikin sojoji na Giwa da ke Maiduguri, kuma an shawo kan lamarin tun karfe 1:30 na safiyar Alhamis.

A cewar Zagazola Makama, a shafin sa na X, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin mazauna garin a daren ranar Laraba, kuma ya samo asali ne daga wani zafi da ya janyo a rumbun ajiyar makamai na bariki, wanda ya kai ga tashin bama-bamai da gobara.

Majiyar ta bayyana cewa, kungiyoyin bayar da agajin gaggawa da suka hada da sojoji da jami’an kashe gobara da sauran hukumomin sun yi aikin cikin dare domin shawo kan lamarin.

Majiyar ta ce “An shawo kan lamarin. Fashe-fashen sun tsaya ne tun da misalin karfe 1:30 na safe, kuma an sanya dukkan matakan tsaro.”

Karin karatu: Hukumar NJC ta dakatar da alkalai 3 na tsawon shekara daya ba tare da biyansu albashi ba, da kuma binciken wasu 27

Majiyar ta kara da cewa “Babu wani hari daga waje, wuta ce ta bazata sakamakon tsananin zafi da ke cikin wani bangare na rumbun ajiyar makamai.”

An rawaito cewa ba a samu asarar rai ba har ya zuwa lokacin da ake cike wannan rahoto, kuma daga bisani al’amura sun koma kamar yadda aka saba.

An yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su yi watsi da jita-jitar harin, domin har yanzu ana samun kwanciyar hankali a duk fadin Maiduguri

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here