Hukumar NJC ta dakatar da alkalai 3 na tsawon shekara daya ba tare da biyansu albashi ba, da kuma binciken wasu 27

njc building

Hukumar kula da harkokin shari’a ta kasa (NJC) ta dakatar da wasu alkalai uku na tsawon shekara daya ba tare da albashi ba.

Alkalan da abin ya shafa su ne mai shari’a Jane E. Inyang na kotun daukaka kara da ke Uyo; Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya dake Abuja, da kuma mai shari’a Aminu Baffa Aliyu na babbar kotun tarayya dake jihar Zamfara.

NJC ta kuma umurci gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, da ya janye nadin mukaddashin babban alkalin jihar, Justice Theophilus Nnamdi Nzeukwu.

Majalisar ta yanke hukuncin a karshen taronta na 108 da ta gudanar a ranakun 29 da 30 ga Afrilu, 2025.

NJC ta kuma bukaci mukaddashin Alkalin Alkalan jihar Imo da ya bayyana mata dalilinsa cikin kwanaki bakwai ko kuma a dauki matakin ladabtarwa a kansa.

Har ila yau, NJC ta bukaci shugaban kotun daukaka kara ta al’ada ta jihar Imo da ya nuna dalilinsa cikin kwanaki bakwai da ya sa ba za a dauki matakin ladabtarwa a kansa ba kan jagorancin taron JSC da ya bayar da shawarar nada mukaddashin alkalin alkalan jihar, sabanin yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Karin karatu: Gwamnan jihar Edo ya tsige sarakunan gargajiya 3

Wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yada labaran hukumar ta NJC, Kemi Babalola ta fitar a ranar Laraba, ta kuma ce majalisar ta kafa kwamitoci 9 da za su binciki jami’an shari’a 27 bisa wasu zarge-zarge na rashin da’a.

Sauran hukunce-hukuncen da majalisar ta yanke sun hada da yin watsi da wasu kararraki 29 da kuma takardar gargadi ga alkalin babban kotun tarayya.

Taron na NJC, wanda babban jojin Najeriya, Hon. Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta jagoranta, ta yanke hukuncin cewa kundin tsarin mulki na nadin mukaddashin Alkalin Alkalan Jiha bai bayar da damar da ya dace ba.

‘’Musamman a kudurin ta, Majalisar ta dakatar da Mai Shari’a Jane E. Inyang na Kotun daukaka kara da ke yankin Uyo na tsawon shekara daya ba tare da biyan albashi ba, saboda kwamitin bincike ya gano cewa ya saba doka ta 3 (5).

”Ka’idojin da’a na Jami’an Shari’a. An samu mai shari’a Jane E. Inyang da laifin cin zarafin ofishinsa ta hanyar bayar da umarnin sayar da Gidan mai na Udemesset da sauran harkokin kasuwanci a matakin tsaka mai wuya na shari’ar.

Karanta: Fadar shugaban kasa ta musanta korar ministoci uku

Haka kuma, Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, shi ma an dakatar da shi na tsawon shekara daya ba tare da biyan albashi ba, sannan kuma an sanya shi cikin jerin wadanda za a sawa ido na tsawon shekaru biyar tare da hana shi samun karin girma har na tsawon shekaru biyar.

Majalisar ta kuma dakatar da Mai shari’a Aminu Baffa Aliyu na babbar kotun tarayya dake reshen Zamfara na tsawon shekara daya ba tare da biyansa albashi ba bisa saba doka ta 3 (1) da na 5 na kundin tsarin shari’a na shekarar 2016.

Har ila yau, ta sanya shi a cikin jerin wadanda za a sanyawa ido na tsawon shekaru uku, domin hana shi samun karin girma.

An samu Mai shari’a Baffa da laifin aikata rashin da’a a shari’a mai lamba FHC/GS/CS/30/2021, gwamnatin jahar Zamfara da EFCC, inda aka zarge shi da bayar da umarnin hana jami’an tsaro gudanar da ayyukansu na ka’ida.

Majalisar ta kuma fitar da wasikar gargadi ga mai shari’a A. O. Awogboro na babban kotun tarayya da ke Legas a wata kara da wani Kasali Azeez Olagoke da S. Hamza suka shigar a kara mai lamba FHC/CS/2021 tsakanin Cif Adesanya Musediku a kan mataimakin janar na ‘yan sanda na Onikan, shiyya ta 2.

An dai yi watsi da karar da aka shigar kan mai shari’a Othman A. Musa na babbar kotun birnin tarayya har sai an yanke hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke daga kara mai lamba FCT/HS/BW/2274/15.

Har ila yau, ta ce an yi rangwame kan karar da wani mai shari’a C. N. Mbonu Nwenyi na babbar kotun jihar Anambra da wani Farfesa Paul C. Obianaso ya shigar bayan bincike ya nuna cewa babu wani rashin da’a daga bangaren alkalan sa.

Sanarwar ta ce, Majalissar ta kuma duba rahoton kwamitinta na tantance koke-koke, wanda ya kunshi jimillar korafe-korafe 43.

‘’Kwamitoci tara ne aka sanya don ci gaba da bincike kan koke-koke 11, yayin da aka kori korafe-korafe 29 saboda rashin cancanta. Koke guda uku akan Hon. Mai shari’a Abubakar Babashani na babbar kotun birnin tarayya, Hon. Mai shari’a Isaac Essien na kotun masana’antu ta kasa, da Hon. Mai shari’a A. O. Musa na babbar kotun birnin tarayya ta Henry Chinweike Okoro, Ikemefuna Stephen Nwoye, Esq.; da Lassborn Chichebem Orjiugo, bi da bi, an saka su a baya har zuwa lokacin da kotun daukaka kara za ta yanke hukunci.

Hukumar ta NJC ta kuma yi la’akari da karar da Mahmud Aliyu ya shigar kan batun nadin alkalai uku a babbar kotun jihar Zamfara.

Mai shigar da karar ya koka da cewa aikin da hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar Zamfara ta gudanar a shekarar 2022, wanda ya kai ga fitar da sunayen ‘yan takarar da aka tantance, bai fito fili ba, kuma ya kasance da son zuciya, da rashin bin doka ta 4, 5, da 6 na dokokin NJC na nadin jami’an shari’a 2014.

Ya kuma yi zargin cewa shugaban hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar Zamfara ne ya zabo wadanda aka nada ba tare da la’akari da ka’idojin NJC na tantance cancanta ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here