Sojoji sun bayyana musabbabin fashewar wani abu a barikin Giwa da ke Maiduguri

Gp0u0vUXgAAjhIp 675x430 (1)

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa a hedkwatar dake arewa maso gabas mai taken Operation HADIN KAI Maiduguri, ta ce ɗaya daga cikin wuraren ajiyar alburusan ta ne da ke barikin Giwa ya fashe da tsakar dare a Maiduguri

Fashewar dai ta faru ne saboda tsananin zafin da ake fama da shi a Maiduguri wanda ya kai ga fashewar wasu alburusai.

Sai dai an shawo kan lamarin tare da hadin gwiwar hukumar kashe gobara ta jihar Borno da sauran motocin kashe gobara daga jami’an tsaro.

An tura dakaru na Operation HADIN KAI domin kare jama’a tare da hana miyagu yin amfani da wannan lamari wajen cimma manufar su.

Labari mai alaƙa: Halin da ake ciki yayin da wani abu ya fashe a Barikin Giwa da ke Maiduguri – Majiyoyin tsaro

Don haka ana kira ga jama’a da su yi watsi da duk wani rade-radin harin da aka kai a karamar hukumar Giwa a Maiduguri, kuma a kwantar da hankula.

Mataimakin Daraktan riko

Jami’in Hulda da Jama’a na Sojoji

Shalkwatar rundunar tsaro ta Operation HADIN KAI

Afrilu 30, 2025

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here