Wani masanin kimiyya a China ya shaida wa BBC cewa bai kamata a yi watsi da batun asalin inda cutar korona ta bullo ba.
George Gao, ya ce har yanzu ba a yi komai a game da matakin gwamnatin China na watsi da batun cewa daga dakin gwaje-gwajen cutukan kasar ta bullo ba.
Ya ce, ”a kimiyyance dole ka zamo mai karbar shawarwari.”
”Ka kasance kana karbar shawara saboda komai zai iya faruwa. Kada ka dauka komai ba zai iya faruwa ba.”
Masanin kimiyyar shi ne shugaban cibiyar kula da cutuka masu yaduwa na China a lokacin annobar korona.
Har yanzu hukumar lafiya ta duniya ta ce ba ta gano ainihin daga ina cutar ta balla ba.
Yawancin masana kimiyya sun ce akwai yiwuwar cutar ta yadu ne daga wajen dabbobi zuwa mutane a birnin Wuhan na China.
Kididdiga dai ta nuna cewa kusan mutum miliyan bakwai ne suka rasa ransu sakamakon cutar korona, ko da yake ana ganin adadin ya iya zarta hakan.













































