Rahotanni da muka samu sun bayyana cewa jami’an hukumar tsaro na farin kaya (DSS), sun hana jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) shiga ofishinsu da ke Ikoyi, jihar Legas. Wata majiya da ba a bayyana sunanta ba ta shaidawa jaridar Premium Times cewa, jami’an tsaron na farin kaya DSS sun toshe ginin baki ɗaya tare da ajiye tankar yaƙi mai sulke a gabansa.
Majiyar ta ƙara da cewa jami’an na DSS sun zo da tankar yaƙi domin tsorata jami’an na hukumar ta EFCC ne.
Sai dai dama an ce a cikin ‘yan kwanakin nan akwai takun-saƙa tsakanin jami’an na hukumar jami’an farin kaya da na EFCC kan batun mallakar ginin.
Har ya zuwa lokacin da ake wannan rahoto, jami’an na DSS sun hana dukkan wani jami’in EFCC da ke ofishin da ke titin Awolowo, Ikoyi shiga wurin.












































