Tsohon shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin jiragen sama, Nnolim Nnaji, ya caccaki tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, saboda jifarsa da ƙarya. Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ɗan majalisar ya bayyana hakan ne a martanin da ya yi kan zargin da tsohon ministan ya yi masa.
Sirika a cikin wata tattaunawa da tashar talbijin ta Arise TV a ranar Lahadi, 11 ga watan Yuni, ya yi zargin cewa ɗan majalisar ya buƙaci da a ba shi kaso 5% na jirgin saman Najeriya.
Hon Nnaji ya nemi da na ba shi kaso 5% na jirgin saman Najeriya domin shi da mutanensa.”
Da yake mayar da martani a ranar Lahadi, ɗan majalisar ya bayyana cewa tsohon ministan ƙarya kawai yake yi masa saboda ya haƙiƙance cewa sai an yi abinda ya dace, cewar rahoton The Punch.
Ya bayyana Hadi Sirika a matsayin wanda ya kusa nutsewa, inda ya ƙara da cewa yana ƙoƙarin tsira ne daga caccakar da yake sha tun bayan ƙaddamar da jirgin saman Najeriya a ƙarshen wa’adin mulkin Shugaba Buhari.
Ɗan majalisar ya bayyana cewa bai kamata ya yi martani kan zargin da ya yi masa ba, amma akwai buƙatar ya yi hakan saboda mutanensa da ƴan Najeriya. “Sirika mutum ne wanda ya kusa nutsewa inda ya ke neman abokin mutuwa domin ya tsira daga caccakar da yake sha tun lokacin da ya ƙaddamar da jirgin saman Najeriya.” A cewarsa.













































