Osinbajo na ganawa da wakilan jam’iyyar APC na Jihar Bauchi

Osinbajo neww.jpg
Osinbajo neww.jpg

Mataimakin shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, na ganawa da wakilan jam’iyyarsu a Jihar Bauchi gabanin zaben fidda wanda zai yiwa jam’iyyar takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023.

Kafin fara ganawar Osinbajo ya ziyarci Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu.

Idan za a iya tunawa dai Mataimakin shugaban Kasar ya ziyarci jihar Gombe, inda ya gana da Gwamnan Jihar da sauran wakilan Jam’iyyar domin neman goyon bayan su a zaben fidda Dan takarar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here