Gwamna Bello Masari ya roki ƴan jihar Katsina su yafe masa

Governor Masari
Governor Masari

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya roki ƴan jihar da su yafe masa na wani abu da ya yi wanda bai yi musu daɗi ba lokacin mulkinsa na tsawon shekara takwas.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da gidan rediyon jihar ya watsa a daren ranar Asabar yayin da yake shirin miƙa mulki ga magajinsa Dikko Umaru Radda wanda shi ne sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar.

Masari ya kuma gode wa ƴan jihar bisa goyon bayan da suka ba shi tsawon mulkinsa.

“Ni ma kamar kowa nake, zan iya yin kuskure, don haka ne ya zama wajibi in nemi gafara daga wajen al’ummar jihar Katsina.

“Fatana da kuma addu’a, shi ne na ganin mutane sun mara wa sabuwar gwamnati da za ta zo. Ina kira ga ƴan Katsina da su saka buƙatun a jihar a farko a kan komai da za su yi,” in ji Masari.

Masari ya ce gwamnatinsa ta taɓa kowane ɓangare na ci gaba a jihar Katsina a tsawon mulkinsa, musamman ɓangaren ilimi, wanda ya ce shi ne yafi bai wa fifiko saboda babu ƙasar da za ta ci gaba ba tare da samun ilimi mai nagarta ba.

Gwamna Masari ya ce yana da yakinin cewa ya yi ɗimbin ayyukan da mutane ba za su ga alfanunsa ba a yanzu, har sai nan da shekaru goma zuwa ashirin masu zuwa, inda ya ƙara da cewa duk abin da gwamnatinsa ta yi, ta yi shi ne domin kyautata rayuwar ƴan jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here