Shugaba Bola Tinubu ya ayyana ranar 7 ga watan Afrilu a matsayin ranar ‘yan sanda ta kasa.
Tinubu, wanda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya bayyana hakan a daren ranar Litinin yayin bikin karramawar da ‘yan sandan Najeriya suka yi a Transcorp Hilton, a Abuja.
Ya bayyana sake fasalin tunanin hukumomi da kuma tunawa da jami’an ‘yan sanda a matsayin wani muhimmin abu a yunkurin gwamnatinsa na mayar da rundunar zuwa cibiya ta zamani, kwararru da kuma rikon amana.
Karin labari: “Ku kare gwamnatin Tinubu ko kuyi murabus” – Matawalle
Ya ce gwamnatinsa ta bullo da sauye-sauye masu yawa domin farfado da rundunar ‘yan sandan kasar tun bayan hawansa ofishi a shekarar 2023.
Don haka ya jadadda bukatar shigar da maza da mata na rundunar wajen horas da su da kuma samar musu da kwararrun da ake bukata domin gudanar da aiki mai wahala na aikin ‘yan sanda na zamani.