“Ku kare gwamnatin Tinubu ko kuyi murabus” – Matawalle

Bello Matawalle, karamin, minista, murabus, tinubu, gwamnati

Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya ce dole ne duk wadanda suka nada Bola Tinubu daga arewa su tashi tsaye domin samun nasarar gwamnatin ko kuma su fice.

Matawalle dai na mayar da martani ne kan sukar kalamansa na farko da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya yi.

Karin labari: TCN ta bayyana dalilan sake maido da wutar lantarki na kasa

Matawalle dai ya caccaki kungiyar Dattawan Arewa da suka yi barazanar cewa Arewa ba za ta zabi Tinubu a 2027 ba, ya kira kungiyar a matsayin takardan siyasa da nauyi ga Arewa.

Sai dai Baba-Ahmed wanda ya taba zama kakakin NEF ya tsawatarwa Matawalle kan yadda ya yi wa kungiyar kakkausar kalamai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here