Kotun koli ta sake tabbatar da hukuncin kisa ga Maryam Sanda, ta soke afuwar da Tinubu ya yi mata

Maryam Sanda and husband 750x430

Kotun kolin kasar nan ta sake tabbatar da hukuncin kisa da aka yanke wa Maryam Sanda, matar ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, saboda laifin kashe mijinta Bilyamin Bello a gidansu da ke Abuja a shekarar 2017.

Tun da farko Babbar kotun Abuja ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 27 ga Janairu 2020 bayan tabbatar da cewa ta kashe mijinta da wuka, abin da ya janyo hukunci mai tsanani daga kotun.

Duk da cewa Maryam Sanda ta shafe kusan shekaru shida da wata takwas a gidan gyaran hali na Suleja, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rage mata hukuncin zuwa shekaru goma sha biyu bisa amfani da ikon zartarwa da tsarin mulki ya ba shi.

Babban lauyan gwamnatin tarayya Prince Lateef Fagbemi ya bayyana cewa an saka sunanta cikin jerin waɗanda aka yi wa afuwa saboda tausayi da kuma la’akari da yaranta, tare da nuna cewa halayenta na kirki, sauyin dabi’a da shiga tsari sun taimaka wajen samun wannan rangwame.

Labari mai alaƙa: Tinubu ya yafewa Maryam Sanda da wasu mutane 174

Kotun koli mai alƙalai biyar ta yanke hukunci da rinjayen mutum huɗu a Abuja, inda ta tabbatar da hukuncin kisa da kotun farko ta yanke, yayin da ɗaya daga cikin alƙalan ya banbanta ra’ayi amma bai sauya sakamakon hukuncin ba.

Kotun ta ce dukkan dalilan da Maryam Sanda ta gabatar domin a soke hukuncin ba su da tushe, tare da tabbatar da cewa an tabbatar da laifinta ba tare da wata shakka ba, sannan hukuncin kotun daukaka ƙara da ya amince da na kotun farko ya tsaya daram.

Kotun koli ta kuma bayyana cewa ba daidai ba ne shugaban ƙasa Tinubu ya yi ƙoƙarin amfani da ikon afuwa ga laifin kisa alhali shari’ar tana gaban kotu, abin da ya sa kotun ta tabbatar da hukuncin kisa da aka yanke tun farko.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here