Tinubu ya ɗaga dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

Bola Tinubu Tinubu Kano 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sanar da ƙarewar wa’adin dokar ta-baci da ya sanyaa a Jihar Rivers tsawon watanni shida, inda ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da kuma ’yan majalisar dokokin jihar za su koma ofis daga Alhamis, 18 ga Satumba, 2025.

A wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ranar Laraba, Tinubu ya ce an sany dokar ta-bacin tun ranar 18 ga Maris, 2025 domin magance matsalar rikicin shugabanci da ya addabi jihar a wancan lokaci.

Shugaban ƙasa ya tuna cewa rikici mai tsanani tsakanin gwamna da wasu ’yan majalisar dokoki 27 da ke goyon bayan kakakin majalisar ya haifar da rashin ingantacciyar gwamnati a Rivers.

Har ma kotun koli ta tabbatar a hukuncinta cewa “babu gwamnati a Jihar Rivers” a lokacin.

Tinubu ya bayyana farin cikinsa da cewa “daga ƙarfe ɗaya na tsakar dare yau, dokar ta-baci a Jihar Rivers ta ƙare.

Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da kuma ’yan majalisar dokokin jihar tare da kakakin majalisa Martins Amaewhule, za su koma bakin aiki daga ranar 18 ga Satumba, 2025.

Tun farko, an kafa dokar ta-bacin ne domin kawo ƙarshen rudanin siyasa da rikice-rikicen doka da suka hana gwamnati gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

Sabuwar sanarwar ta kawo ƙarshen wani babi na rikice-rikicen siyasa da ya hana Jihar Rivers samun daidaito na tsawon watanni.

Shugaban ƙasa ya ce gwamnati za ta ci gaba da sa ido kan lamarin domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da tsari a jihar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here