Akantocin IPPIS sun amsa laifin karkatar da albashin tsoffin ma’aikata

Court Gavel

Wata kotun tarayya da ke Legas ta dage sauraron shari’ar ma’aikata biyu na tsarin biyan albashi na ma’aikata (IPPIS) da ake tuhuma da karkatar da albashin tsoffin ma’aikata a cibiyar lafiya ta tarayya da ke Ebute Meta, har zuwa 18 ga Satumba domin nazarin hujjoji.

Mutanen da ake tuhuma su ne Shola Onasanya, babban akawu, da Halimat Olalere, jami’ar kula da lissafi.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ƙasa (ICPC) ce ta gurfanar da su gaban mai shari’a Ibrahim Kala bisa tuhuma mai ɗauke da laifuka guda biyu da aka gyara.

A zaman kotun na Laraba, lauyan gwamnati Enosa Omoghibo ya shaidawa kotu cewa wadanda ake tuhuma sun shiga yarjejeniyar sasanci, kuma saboda haka aka gabatar da sabon tuhuma domin karantawa a gaban kotu.

Sai dai alkali ya tunatar da lauyan gwamnati cewa dole ne kotu ta amince kafin a shigar da sabon tuhuma.

Daga bisani, bayan amincewar bangarorin biyu, an karanta musu tuhumar inda suka amsa da laifi.

Kotun ta kuma nuna cewa duk da amincewar wadanda ake tuhuma da laifi, dole ne gwamnati ta gabatar da wasu shaidu kafin a yanke hukunci, domin amsa laifi kawai ba zai wadatar wajen tabbatar da hukunci ba.

A cewar tuhumar, ma’aikatan sun aikata laifin ne tsakanin Janairu da Disamba na shekarar 2023, inda suka karkatar da sama da naira miliyan 1.17 ta hanyar ci gaba da karɓar albashin tsoffin ma’aikata, sannan suka juya kudaden zuwa asusunsu na kansu.

Hukumar ICPC ta shaida wa kotu cewa Olalere ta karɓi kudaden a asusunta, sannan ta rika tura wa Onasanya bisa umarninsa, lamarin da ya saba da dokar hana wanke kudi ta shekarar 2022.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here