Wanda ake zargi da yin garkuwa Hanifa Abubakar, ƴar shekara 5, Abdulmalik Tanko ya musanta zargin, inda ya bayyana bai aikata laifin ba.
Kisan Hanifa: Wanda ake zargi Abdulmalik Tanko ya musanta yin garkuwa da kuma kashe ta
Wanda ake zargi da yin garkuwa Hanifa Abubakar, ƴar shekara 5, Abdulmalik Tanko ya musanta zargin, inda ya bayyana bai aikata laifin ba.
Abdulmalik Tanko ya musanta zargin ne a yayin zaman kotun na yau litinin wadda mai sharia Usman Na-Abba ke jagoranta.
Haka kuma ita ma dayar wadda ake zargi Fatima Jibrin, ta musanta zargin da aka karanto mata.
Shima Hashimu ya musanta zargin garkuwa da Hanifa da ba ta guba da kuma binne gawarta a wata makaranta kamar yadda aka ganu su a bidiyo suna amsawa tun da farko.
Sai dai sun amsa zargi ɗaya cikin uku da aka karanto musu, wanda shi ne na haɗa baki..
Lauyoyin gwamnati ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Shari’a Barista Musa Lawan sun nemi kotu ta ba su damar kawo shaidunsu a zama na gaba.
Mai Shari’a Usman Naabba ya ɗage zaman kotun zuwa 2 da 3 ga watan Maris mai zuwa don sauraron shaidu.













































