Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta ki amincewa da karawa Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Isa Ibrahim Pantami matsayin Farfesa a fannin tsaro ta yanar gizo da hukumomin Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri (FUTO) suka yi.
Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a wani taron manema labarai a Legas a karshen taron kwanaki biyu na majalisar zartarwar kungiya ta kasa ta yi (NEC).
Ya bayyana karin girma a matsayin ‘wanda aka yi ba bisa doka ba.’
Idan za’a iya tunawa Pantami yana cikin malamai bakwai da jami’ar FUTO ta daukaka zuwa matsayin farfesa a taronta na shekara-shekara karo na 186.
Shugaban ASUU ya ce: “Yan uwa ‘yan jarida, za ku iya tuna cewa kungiyarmu ta cire kanta daga nadin Dr Ibrahim Pantami a matsayin farfesa a fannin tsaro ta yanar gizo da Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri (FUTO) ta yi a yayin taron mu da aka gudanar a Jami’ar Abuja a ranakun 18-19 ga Nuwamba, 2021, har sai wata tawagar binciken gaskiya da za a aika zuwa jami’ar ta bayar da rahoton binciken ta.
“Tawagar ta ziyarci jami’ar ne a ranakun 10-14 ga Fabrairu, 2022, kuma ta kawo ga rahoto ga hukumar zartarwa ta kungiyar. Sakamakon cikakken rahoton da aka gabatar a kan dukkan abubuwan da suka dace, Hukumar zartarwa ta kungiyar ta ki amincewa da nadin Dakta Isah Ali Ibrahim Pantami a matsayin Farfesa a fannin tsaro na Intanet.
“Daga shaidun da muke da su, Dokta Pantami bai cancanta ba, kuma nadin da aka yi ya saba wa ka’idojin da aka kafa na nadin malaman jami’a.”
“NEC ta umurci daukacin mambobin kungiyarmu da rassan kungiyarmu a fadin tarayyar Najeriya da kada su amince, ko kuma su dauki Dokta Isah Ali Ibrahim Pantami a matsayin farfesa a harkar tsaro ta yanar gizo ta kowace hanya.
“NEC ta kuma kuduri aniyar hukunta duk ‘yan kungiyar ASUU da suka shiga aikin wanda ya kai ga nadin ba bisa ka’ida ba bisa ka’idojin kungiyar mu.”