Hukumar NYSC mai kula da masu yi wa kasa hidima ta karawa wasu Mambobi 40 wa’adin hidimar kasar sakamakon kauracewa wuraren da aka tura su na ainihi a Jihar Nasarawa.
Mista Abdullahi Jikamshi, Ko’odinetan hukumar na jihar, shi ne ya bayyana hakan yayin bikin yaye masu hidimar kasa na shekarar 2021 ‘Yan rukunin ‘A’ kashi na ‘2’ (Batch -A- Stream-2) ranar Alhamis a Lafiya.
A cewarsa, Mambobin da abin ya shafa sun kasa bin tsarin hukumar, inda suka kaurace wa wuraren da aka turasu domin yin hidimar kasar.
Jikamshi ya bayyana cewa, jimillar matasa dubu 1 da 853 da suka yi wa kasa hidima a jihar za a ba su takardar shaidar kammala hidimar kasa.
Ko’odinetan ya kuma sanar da cewa mutane 3 ne ‘Yan rukunin -A- kashi na 2 suka mutu a wannan shekarar.
Kazalika ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya kuma jajantawa iyalansu inda kuma ya kara da cewa, “sun bayar da babbar gudunmawa wajen yi wa kasa hidima.”
Jikamshi ya mika godiyarsa ga gwamnatin jihar da majalisar sarakunan jihar da sauran jama’a bisa yadda suke ci gaba da bayar da goyon baya don tabbatar da tsaro da samun nasarar ‘masu yiwa kasa hidima a duk lamuransu.













































