Gwamnatin jihar Kaduna ta soke sayar da gidaje da filaye a wasu tsofaffin makarantun gwamnati da suka hada da Queen Amina College, Kwalejin Alhuda-Huda, Zariya; da Government Commercial College, Zaria.
Wannan shawarar ta yi daidai da kudurin gwamnati na bunkasa rayuwar al’umma da kuma manufarta na tabbatar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa a makarantu.
Sakataren gwamnatin jihar Kaduna, Dakta AbdulKadir Mu’azu Meyere, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce an amince da soke sayarwar ne a shekarar da ta gabata, kuma ana daukar matakan dawo da kudaden da aka biya.
“Gwamnatin jihar Kaduna a karkashin jagorancin mai girma Sanata Uba Sani ta soke duk wani siyar da gidajen makarantu da aka yi a baya domin cimma muradun jama’a da kuma amfanar da su” in ji Meyere.
Ya kara da cewa gwamnati ta yi imanin cewa ingantaccen koyo zai iya faruwa ne a cikin yanayi mai kyau.
Gwamna Uba Sani ya jaddada mahimmancin ilimi a matsayin tsani tare da ikon canza rayuwa da inganta rayuwa.
Karin karatu: Kwara: Yan bindiga sun kashe ɗan banga da wasu mutane 6
A cewar sanarwar, gwamnan ya yi ta kokarin fadada hanyoyin samun ilimi ta hanyar magance matsalar karancin ababen more rayuwa a makarantun firamare da sakandare.
“Wasu daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin jihar Kaduna ta aiwatar sun hada da gina sabbin ajujuwa sama da 2,336, gyara sama da ajujuwa 707, da samar da abin zama guda 3,704 ga malamai, da kuma guda 30,742 ga dalibai.
Meyere ya kara da cewa “Gwamnati ta kuma haƙa rijiyoyin burtsatse guda 51 tare da samar da bandakuna 918 ga dalibai da malamai.”