Flying Eagles ta doke kasar Egyp a shirye-shiryen fara tun karar gasar AFCON

Flying Eagles

Kungiyar kwallon kafa ta Nigeriya ta Matasa yan kasa da shekaru 20 Flying Eagles, ta doke kasar Egypt da ci 2-1 a wasan sada zumunta da suka gudanar a ranar Talata 22/04/2025 a kasar ta Egypt.

Wasan na a matsayin wasan gwaji na shirye shiryen tunkarar gasar cin kofin Afrika yan kasa da shekaru 20 da za a gudanar a kasar ta Egypt.

kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa za a fara gudanar da gasar a ranar Lahadi 27 ga watan da muke ciki na Afrilu a kasar ta Egypt.

Za kuma a karkare ta a ranar 18 ga watan Mayu mai kamawa.

A mintuna 10 da fara wasan dan wasan Najeriya Kparobo Arierhi ya zura kwallo a ragar kasar Egyp kafin daga bisani dan wasan kasar ta Egpt Ahmed Kaabaka, ya warware kwallon a mintuna na 65, sai dai a mintuna na 83 Precious Benjamin daga Najeriya ya kara kwallo ta biyu a bugun daga kai sai mai tsaran raga a haka kuma aka tashi wasan.

Super Falcon daga Najeriya dai tafi kowacce kungiya yawan daukar gasar inda take da ita guda 16 idan har ta dauki wannan zai kasance ta dauka sau 17.

A karshen gasar dai za a fitar da kasashen da suka kare daga na 1 zuwa na 3 inda za su wakilci Afrika a gasar cin kofin Duniya ta Matasa yan kasa da shekaru 20 da za a fafata a kasar Chile daga ranar 27 ga watan Satumba zuwa ranar 19 ga watan Oktoba (NAN).

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here