Ma’aikatan Jihar Zamfara Sun Gudanar Da Salloli Na Musamman Kan Rashin Biyan Albashi 

Zamfara 4 750x430 1
Zamfara 4 750x430 1

Wasu ma’aikatan gwamnatin jihar Zamfara sun gudanar da Salloli na musamman, a masallacin idin Gusau, babban birnin jihar ranar Asabar.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ma’aikatan sun taru a masallacin idin ne da misalin ƙarfe 10 na safe, inda suka nemi Allah ya kawo mu su ɗauki kan kuɗaɗen albashinsu.

Ma’aikatan sun bayyana cewa, rabon da a ba su albashi tun watan Janairu, wanda hakan ya jefa su cikin halin ƙaƙanikayi.

Wani daga cikin ma’aikatan wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa da kyar su ke iya samun abun sanyawa a bakin salati.

Ya ce wannan Sallar da suka yi, sun yi ta ne domin neman taimako wajen Allah, ya sanya gwamnan jihar da duk wasu masu ruwa da tsaki, da su tausaya mu su, su ba su ƴan haƙƙoƙinsu.

A kalamansa: “Da yawan mu mun kusa fara bara, ba mu iya samun abinda za mu ci ko sau ɗaya a rana. Wannan Sallar ta musamman ta mu ka gudanar, mun yi ta ne domin neman Allah ya sanya gwamnan mu, ƴan majalisar dokoki da duk wasu masu hannu a ciki, da su ji tausayin mu.”

“Mun sha wuya sosai a dalilin wannan ƙangin da mu ka tsinci kan mu, wasu da da yawa sun rasa rayukan su, ba mu son hakan ya cigaba da faruwa. Mun taru a nan ne ba tare da la’akari da bambancin addini ba domin neman Allah ubangiji ya kawo mana ɗauki.”

Ƙoƙarin jin ta bakin gwamnatin jihar, kafin kammala haɗa wannan rahoton ya ci tura, domin layin wayar kwamishinan watsa labarai na jihar, Ibrahim Dosara, a rufe ya ke.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here