Fursunoni sun shiga yajin cin abinci a Iran

1684695452349
1684695452349

Wata kungiyar kare hakkin ɗan adam a Iran mai suna Harana, ta ce wasu fursunoni da ke gidan yarin Ghazalhasar sun shiga yajin cin abinci sakamakon yawan zartas da hukuncin kisa kan fursunoni da ake yi a ƙasar a baya-bayan nan.

Fursunonin sun fara yajin cin abinci ne a yau Lahadi don adawa da batun ƙaruwar zartas da hukuncin kisa da hukumomin Iran ke yi, inda suka ki karɓar abinci da gidan yarin ke ba su.

A baya-bayan nan, ana samu ƙaruwar zartas da hukuncin kisa kan fursunonin siyasa da kuma waɗanda ba na siyasa ba a ƙasar ta Iran.

Batun zartas da hukuncin kisan ya gamu da martani daga ɓangarori da dama a faɗin duniya tare da gudanar da zanga-zanga a wasu biranen ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here