Mataimakin sakataren labaran APC na kasa ya yi murabus, ya fice daga jam’iyyar.

Mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC mai mulki ta kasa Murtala Ajaka ya yi murabus tareda ficewa daga jam’iyyar.

Murabus din Mista Ajaka na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu, kuma mai kwanan wata 17 ga Mayu.

Mista Ajaka, a cikin wasikar, ya ce ya kuma aike da wasikar a rubuce ga shugaban jam’iyyar APC, na mazabar Ajaka dake karamar hukumar Igalamela/Odolu a jihar Kogi.

Ko da yake bai bayyana dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar ba, amma hakan ba zai rasa nasaba da rikicin baya-bayan nan da ya barke a zaben fidda gwani na APC a Kogi a watan Afrilu ba.

Tsohon mataimakin sakataren yada labaran na cikin wadanda suka ki amincewa da takarar gwamnan da aka nada, Usman Ododo.

Wasikar ta ce, “Na rubuto ne domin in sanar da kai da kuma kwamitin ayyuka na kasa na babbar jam’iyyarmu ta APC, shawarar da na yi na yin murabus daga mukamina na mataimakin sakataren yada labarai na kasa da kuma mamba a jam’iyyar APC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here