Jami’an runduna ta musamman a hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) sun cafke manyan dillalan ƙwayoyi guda biyu, Victor Nwosa da Felix Chika Obiegbu, bayan gano tarin kwayoyin cocaine, heroin da methamphetamine da suke shirin fitarwa zuwa Turai da wasu ƙasashe.
Bayan watanni ana bincike da sa ido, jami’an NDLEA sun mamaye gidajensu a Lagos, inda aka gano kayan mayen.
Nwosa mai shekara 64 ya dade yana bayyana kansa a matsayin ɗan kasuwar kayan ɗinki, yayin da Obiegbu mai shekara 49 ya shahara da kasuwancin ruwan inabi, duk da cewa asalin sana’arsu ta boye ita ce fataucin miyagun ƙwayoyi.
Karanta: NDLEA ta ba da shawarar a tilasta yin gwajin miyagun ƙwayoyi ga masu neman lasisin tuƙa mota
Sanarwar da daraktan yada labarai da yaƙin neman goyon bayan jama’a na NDLEA, Femi Babafemi ya fitar a ranar Lahadi a Abuja ta bayyana cewa an kama Nwosa a gidansa da ke Okota a ranar 17 ga Satumba, inda aka gano kilo 4.33 na heroin da gram 448 na cocaine.
Shi kuma Obiegbu, an kama shi a gidansa da ke Aguda, Surulere a ranar 11 ga Satumba, inda aka gano kilo 2.902 na methamphetamine.
Hukumar ta kuma bayyana cewa an hana wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi da ake zargi da tallafawa ‘yan ta’adda da ‘yan fashi a Borno da Yobe jigilar kwayoyi da aka ɓoye cikin motoci da jaka.
A Borno, an cafke wani matashi mai suna Baba Kaka Ibrahim da motar Mercedes-Benz GLK inda aka gano kwayoyi sama da 39,000 na tramadol da Exol-5.
Karin labari: NDLEA ta kama ’yan Najeriya biyu da suka dawo daga Brazil da hodar iblis da koken
A Yobe kuma, wata mata Halima Adamu an kama ta da kilo 1.4 na Colorado a jakarta, lamarin da ya kai ga kama wata mata mai hannu a ciki, Habiba Muhammad.
A Kano, jami’an NDLEA sun kama matasa biyu, Aliyu Sani da Yahaya Tata, da kwayoyi fiye da 30,000 na tramadol.
Haka kuma a Bayelsa, an kama wasu mutum uku da kilo 12 na skunk da harsashi 50.
A Ekiti, an kama wani tsohon ɗan gidan yari, Femi Owoeye, da kilo 32 na skunk da wasu kwayoyi a gidansa.
Haka zalika a Kaduna, jami’an NDLEA sun kama wani mutum da sunan Adedamola Olayeni da kilo 262.6 na skunk a motarsa, yayin da aka kama wani Zubairu Haruna da gram 506 na methamphetamine.
An kuma gano cewa shi ma yana da hannu wajen aika kayayyakin zuwa Gombe inda aka cafke abokin harkallarsa, Babangida Mohammed.
Binciken ya kuma haifar da kama wasu mutane a Lagos, Abuja da Edo, inda aka lalata gonaki da dama na tabar wiwi da kuma kwace kayan da nauyinsu ya kai ton da dama.
Hukumar NDLEA ta jaddada cewa tana ci gaba da aikin fatattakar masu safarar miyagun ƙwayoyi da murkushe sana’arsu a dukkan sassan ƙasar.












































