Matatar Man Ɗangote: PENGASSAN sun fara yajin aiki a faɗin ƙasa sakamakon korar ma’aikata da kamfanin ya yi

PENGASSAN

Ƙungiyar ma’aikatan manyan jami’an man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta bayyana fara yajin aikin ƙasa baki ɗaya, biyo bayan sallamar ma’aikata 800 da kamfanin sarrafa mai na Dangote ya yi ba bisa ƙa’ida ba saboda shiga ƙungiyar.

Sanarwar hakan ta fito ne daga wata takarda da ta biyo bayan taron gaggawa na majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) na ƙungiyar a ranar Asabar, 27 ga Satumba, 2025, wadda babban sakataren ƙungiyar, Lumumba Okugbawa ya rattaba hannu a kai.

Sanarwar ta umarci mambobinta da su daina aiki daga Lahadi, 28 ga Satumba, kafin a kammala da cikakken dakatar da ayyuka a dukkanin kamfanoni, cibiyoyi, hukumomi da ofisoshin man fetur da iskar gas daga Litinin, 29 ga Satumba.

Ƙungiyar ta ce dukkan mambobin PENGASSAN a wuraren aiki su dakatar da ayyuka daga ƙarfe 6:00 na safe ranar Lahadi, tare da shiga addu’o’i na awa 24.

Wannan ya haɗa da ayyukan dakunan sarrafawa, na’urorin kulawa da kuma ma’aikatan filaye.

PENGASSAN ta kuma yi zargin cewa kamfanin ya maye gurbin waɗanda aka sallama da sama da Indiyawa 2,000, tana kiran wannan abu a matsayin barazana ga ma’aikatan Najeriya baki ɗaya.

Karin labari: PENGASSAN ta dakatar da kai iskar gas zuwa Kamfanin Mai na Dangote

Ƙungiyar ta umarci dukkanin reshen kamfanonin mai su dakatar da samar da iskar gas da mai zuwa masana’antar Dangote nan take, sai dai a wuraren da ke da alaƙa da tsaron ma’aikata da kadarori, inda ake buƙatar izini daga sakatariyar ƙasa.

Sai dai masana’antar Dangote ta musanta zargin sallamar ma’aikata da yawa, tana mai cewa tana aiwatar da gyaran cikin gida ne domin ƙara inganci, tare da jaddada cewa mafi yawan ma’aikatanta ‘yan Najeriya ne.

Rigimar ta samo asali ne daga wasikar da kamfanin ya aikawa wasu ma’aikata a ranar 24 ga Satumba, inda ya zarge su da yi wa tsaron aiki barazana.

Amma PENGASSAN ta dage kan cewa sallamar mutane sama da 800 ba bisa ƙa’ida ba aka yi, tana kira ga gwamnati da sauran ƙungiyoyin ƙwadago da su shiga tsakani.

Wannan rikici ya ƙara ta’azzara rashin jituwa tsakanin kamfanin da ƙungiyoyin ma’aikatan man fetur, inda har ma ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (NUPENG) ke cikin rikici da kamfanin kan batun haƙƙin ma’aikata da matakan tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here