Naira miliyan 100 da aka tura asusun dan Egbetokun kuskure ne — Kakakin ’Yan Sanda

Benjamin Hundeyin 750x430

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ce tura Naira miliyan 100 cikin asusun Victor Egbetokun, dan tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, kuskure ne aka yi.

Bayanin ya biyo bayan wani rahoto da ya yadu a kafafen sada zumunta cewa an tura kudin daga asusun kudin tsaro na Gwamnatin Jihar Anambra.

Da yake magana a wani shirin siyasa a gidan talabijin ranar Litinin, Kakakin Rundunar ’Yan Sanda, Benjamin Hundeyin, ya ce Victor ya sanar da ’yan sanda faruwar lamarin, kuma aka mayar da kudin nan take.

Ya ce an fitar da takardar bayanin mu’amalar asusun, wadda ta nuna cewa an mayar da Naira miliyan 100 din.

A cewarsa, ana ganin kudin a cikin asusun, sai aka tuntubi jami’in kula da asusun domin mayar da su, kuma aka kammala hakan ba tare da bata lokaci ba.

Ya kuma ce an rufe asusun, sannan an kai korafi ga hukumar da ke yaki da cin hanci domin a binciki zargin.

Hundeyin ya bayyana lamarin a matsayin kuskuren hada-hadar kudi, inda aka mayar da kudin cikin asusun gwamnatin jihar jim kadan bayan gano abin da ya faru.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here